Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan bindiga Sun Sace Dalibai A Delta


Wani dan bindiga a Najeriya
Wani dan bindiga a Najeriya

“Rundunar ‘yan sanda na sane da wannan mummunan al’amari, muna kuma daukan dukkan matakan da suka dace don ganin an kubutar da su ba tare da sun jikkata ba.”

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta da ke kudu maso kudncin Najeriya ta tabbatar da sace wasu dalibai da ba a kammala tantance adadinsu ba.

Kakakin ‘yan sandan Edafe Bright ya fada a wani sakon X da ya wallafa a shafinsa cewa, rundunar na sane da wannan a'lamari.

“Rundunar ‘yan sanda na sane da wannan mummunan al’amari, muna kuma daukan dukkan matakan da suka dace don ganin an kubutar da su ba tare da sun jikkata ba.”

Rahotannin sun ce daliban na tafiya ne cikin wata ‘yar karamar motar bas a yankin karamar hukumar Ughelli a ranar Juma’a.

Gidan talbijin na TVC ya ruwaito cewa daliban sun kai su goma.

Kakaki Bright ya ce ba a tuntubi kowa kan neman biyan kudin fansa ba amma suna iya bakin kokarinsu don ganin an ceto daliban.

Matsalar satar mutane domin neman kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya musamman a arewacin kasar, inda ‘yan bindiga kan kaikaici dalibai, mata da yara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG