Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Biciken Wata 'Yar Sanda Da Ake Zargi Da Satar Yara 5 A Sokoto


Nigeria Police Force Logo
Nigeria Police Force Logo

Yaran masu kananan shekaru ciki har da jinjira wadda bata wuce 'yan makonni ba da haihuwa, an sace su daga Sakkwato aka kai su babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, kafin dubun wadanda ake tuhuma ta cika.

Rundunar 'yan sandan Najeriya na kan binciken zargin satar yara biyar da ake tuhumar wata mata 'yar sanda ASP Kulu, da wata Elizabeth da hannu ciki.

An kama ASP Kulu da Elizabeth a Abuja bayan da fasinjojin da suka shiga mota daya da su daga Sakkwato suka kyankyasawa jami'an tsaro cewa suna tuhumar matan biyu.

Abba Dan Baba, wanda yana cikin motar yace tun a Sakkwato ASP Kulu ta je tashar mota ta biya kudin fasinja uku tace sauran biyu suna kan hanya za'a tsaya a dauke su, kuma da aka je Kasarawa sai aka dauki yara kanana biyar da Elizabeth.

Yace daga cikin yaran akwai jijnjira wadda bayan an dauke su a mota ta yi ta faman kuka, kuma aka kasa ba ta mama, daga nan ne wasu mata dake cikin motar suka soma lura da akwai rashin kyakkyawar alaka tsakanin yaran da matan da suka dauko su, sai suka sanar da sauran fasinjoji, bayan da suka sauka Abuja, aka sanar da 'yan sanda suka kama su.

Kwamred Nura Muktar Kanya mataimakin jami'an gudanarwa na gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama a Abuja yace sun samu labarin aukuwar hakan ne daga jama'a sai suka garzaya caji ofis ta 'yan sanda da aka tsare matan biyu.

Bayan gudanar da bincike aka mayar da su babban ofishin 'yan sanda inda daga baya aka mayar da batun zuwa ga rundunar 'yan sanda ta Sakkwato.

Jami'in gudanarwa na gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama a Sakkwato Sirajo Madawaki yace sun karbi batun daga reshen su na Abuja kuma suna kan bibiyar batun a Sakkwato da yake an kawo wadanda ake tuhumar.

Yace ba zasu yi kasa a guiwa ba sai sun ga an kammala bincike an hukunta masu laifi an mayar da yaran a hannun iyayensu.

Rundunar 'yan sanda ta jihar Sakkwato ta bakin kakakinta ASP Ahmad Rufa'i tace da ma batun take jira a turo daga Abuja kuma yanzu ya iso zasu dora daga inda aka tsaya.

Wannan lamarin na ci gaba da kasancewa babban abin mamaki ga jama'a musamman duba da samun hannun jami'ar 'yan sanda a ci ciki, abinda ya sa suke ganin yana da kyau a sanya ido sosai ga yadda lamarin zai kaya.

Batun satar yara daga wani yanki zuwa wani a Najeriya ya jima yana ci wa mautane tuwon a kwarya domin an sha samun irin wadannan matsoliolin da ake satar yara daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya, kamar wanda jami'an DSS suka mayar da wasu yara 4 daga aka sace daga jihohin Sakkwato da Kebbi a watan janairun 2022.

A saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:

An Fara Biciken Wata 'Yar Sanda Da Ake Zargi Da Satan Yara 5
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG