Kakakin ‘yan sandan jihar, Bright Edafe, ne ya tabattar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin.
“An ceto duk tara da aka sace" inji Kakakin.
Rahotannin na nuni da cewa an sace daliban ne yayin da suke tafiya cikin wata ‘yar karamar motar bas a yankin karamar hukumar Ughelli a ranar Juma’a.
Yayin da ya ke tabbatar da afkuwan lamarin, ya ce “Rundunar ‘yan sanda na sane da wannan mummunan al’amari, muna kuma daukan dukkan matakan da suka dace don ganin an kubutar da su ba tare da sun jikkata ba.”
Hakan na zuwa ne jim kadan bayan aka sace dalibai 137 daga wani makarantar firamare a kauyen Kuriga a jihar Kaduna.
Matsalar satar mutane domin neman kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya musamman a arewacin kasar, inda ‘yan bindiga kan kaikaici dalibai, mata da yara.
Dandalin Mu Tattauna