Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyi Biyu Sun Kori Masu Horas Masu Da 'Yan Wasa


kungiyar kwallon Kafa ta Leeds United ta kori kocin ta Thomas Christiansen bayan watanni takwas da kama aiki, kungiyar ta Leed, ta ce Kocin mai shekaru 44 ya kasa tabuka wani abin kirki domin kuwa kungiyar ta buga wasanni 30, amma da kyar ta sami nasara a guda 13 kacal, ciki harda rashi nasara da ya yi a gasar FA Cup inda kungiyar Newport County. Ta yi waje road da ita a gasar bana.

Kungiyar ta Leed, yanzu haka zata nemi manaja na bakwai kenan a kungiyar tun daga shekara ta 2014 zuwa 2018.

Ita ma Deportivo La Coruna, ta Sallami kocinta Cristobal Parralo, Kungiyar ta ce kocin ya kasa tabuka abin azo a gani a kungiyar inda ya buga wasanni bakwai a jere na Laliga, amma maki biyu kacal ya samu.

A ranar Jumma'a ne Real Sociedad, ta lallasa ta da kwallaye 5-0 a wasan mako na 22 na Laliga, a yanzu haka dai kungiyar tana mataki na 16 ne a teburin Laliga mako na 22.

Alexis Sanchez, ya zura kwallon sa ta farko a kungiyar Manchester United a wasan da suka buga tsakaninsu da Huddersfield na Firimiya lig mako na 26, Sanchez ya sami wannan nasara ce a cikin mintuna na 68 da fara wasan, Lukaka shi ya fara taba raga a minti na 55, an tashi a wasan 2-0.

Wannan Lamari ya janyu Huddersfield town ta samu kanta acikin jerin kungiyoyi masu zuwa Relegations inda take mataki na 19 da maki 24, Shima sabon dan wasan Kungiyar Arsenal, Aubameyang ya jefa kwallon sa ta farko a wasansa na farko wa kungiyar ta Arsenal.

A wasan da Arsenal ta lallasa Everton da ci 5 - 1 na Firimiya lig, Aubameyang ya sami nasara ne a cikin mintuna na 37 da fara wasan kafin tafiya hutun rabin lokaci inda aka tafi hutun rabin lokaci 4-0.

Shi kuwa Mkhitaryan, da shima ya zo a watan janairu daga Manchester united ne ya taimaka wajan shigar kwallaye 3 da aka ci, ciki harda wadda Aubameyang yasha an tashi wasan da kwallaye 5-1.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:16 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG