Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Flying Eagle Ta Gaza Kai Ga Wasan Karshe Bayan Ta Sha Ci Daya Mai Banhaushi A Hannun Gambia


Super Eagles
Super Eagles

Tawagar ‘yan wasan Flying Eagles ta Najeriya ta gaza kai wa wasan karshe a gasar cin kofin Afrika ta matasa 'yan kasa da shekaru 20 na 2023 bayan da ta sha kashi da ci daya mai banhaushi a hannun Young Scorpions na kasar Gambia.

Adama Bojang ne ya zura kwallo da ta kai Gambia ga yin nasara, mintuna bakwai bayan kuskuren kyaftin din Flying Eagles, Daniel Bamaiyi.

Wannan shine harbi daya tilo da Gambia ta samu a tsawon lokacin wasan.

Flying Eagles sun fafata sosai don ganin ta barke kwallon amma hakar ta bata cimma ruwa ba saboda rashin kwarewa a wasan karshe na uku.

'Yan wasan Najeriya (Facebook/NFF)
'Yan wasan Najeriya (Facebook/NFF)

‘Yan wasan na Ladan Bosso sun samu bugun fenareti saura minti shida a tashi wasan bayan da aka yi wa Ahmed Abdullahi rauni wanda ya shigo wasan daga baya a cikin akwatin abokan karawan su.

Dan wasan gaba na KAA Gent ya buga fenareti kwallon ta kauce ta daki katako, lamarin da ya jefa abokan wasansa cikin dacin rai.

An rage Gambia zuwa mutum 10 a makararren lokacin da aka fidda Haruna Njie a kalubalen da ake yi masa.

Kungiyar Flying Eagles za ta kara da Tunisia a wasan neman gurbi na uku a ranar Juma'a.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG