Dan wasan da ya shigo bayan hutun rabin lokaci shine ya girgiza raga daga bugun tazara na kusan karshen wasan da ya baiwa bangaren Chris Hughton nasara a wasansa na farko matsayin kocin Black Stars.
Nasarar ta sa Ghana ta zama ta daya a rukunin E bayan ta samu maki bakwai a wasanni uku da Angola da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da dukaninsu ke da maki hudu hudu.
Mohammed Kudus ne ya fara samun dama ta farko a Black Stars amma dan wasan tsakiyar na Ajax ya kasa zura kwallo inda ya daga kwallo ta yi sama sosai bata yi kusa da raga ba.
Dan wasan Angola Gelson Dala ya tilastawa Golan Ghana Lawrence Ati-Zigi yin tsalle ya buge yayin da ya aiko da kwallo a kusa da akwatin Ghana.
‘Yan wasan Angola sun hana Kudus zura kwallo ne a mintuna na 18 da 27, inda golan Angola, Neblu, ya kara kaimi.
Yayin da Black Stars suka samu damarmaki a farkon rabin wasan, sun gaza kada raga inda zagayen farko ya kare wanda babu ci kwallo.
Ko a zagaye na biyu wasan bai yi wa Ghana kyau ba yayin da bangaren Hughton ke fafutukar ganin ta doke abokan karawan su dake suka bakwanci Kumasi.
Sai dai kuma saura minti daya a tashi daga wasan, Semenyo ya mayar da martani da sauri ga kwallon da ta fado gabansa a cikin akwatin 18, inda ya zura kwallon da ta baiwa Ghana nasarar da take bukata.
Yanzu dai ‘yan wasan Black Stars za su maida hankali a wasansu na gaba a ranar Litinin 27 ga Maris, lokacin da za su je birnin Luanda don karawa da Angola.
-Hotuna daga Hukumar GFA