Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fafutukar Ballewa Daga Najeriya; Buhari Ya Amince A Hau Teburin Sulhu


Shugaban Najeirya, Muhammadu Buhari (Instagram/ Muhammadu Buhari).
Shugaban Najeirya, Muhammadu Buhari (Instagram/ Muhammadu Buhari).

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince a hau teburin sasantawa da 'yan kabilar Igbo, da ma duk wadanda ke fafutukar ballewa da raba kasar.

Ministan kwadagon Najeriya Chris Ngige ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a hau teburin sulhu, domin sasantawa da masu fafutukar ballewa daga kasar a yankin kudu maso gabas.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa ta Aso Rock jim kadan bayan gudanar da wani taron tattaunawa akan matsalar da shugaban kasa, Chris Ngige ya ce sun yi la'akari ne da yanayin tabarbarewar tsaro, suka kuma shawarci shugaban kasa dangane da bukatun jama'ar yankin da kuma na gwamnati.

Chris Ngige
Chris Ngige

Ngige ya ce "muna son bin tafarkin sulhu. wajibi ne mu tsaya mu tattauna tare da yin nazari, wanda kuma za mu fara daga Litinin din nan."

Ya ce tuni da gwamnatin tarayya ta tsara hanyoyin tunkarar lamarin, ta yadda za'a cire tunanin "kyama" da ta cikin zukatan 'yan kudu maso gabas a Najeriya.

Ministan ya ce wasu takwarorinsa da suka hada da ministan tsaro, da na lamurran cikin gida da kuma manyan hafsoshin tsaro sun ziyarci yankin a ranar Assabar da ta gabata, "kuma za mu dora da tattaunawa daga inda suka tsaya."

Karin bayani akan: Chris Ngige, Muryar Amurka, IPOB, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Ya ci gaba da cewa "mun bayyanawa shugaban kasa kuma ya amince da cewar sulhu ne kawai mafita. Kamar yadda na sha fada, wajibi ne mu yi la'akari da yanayi, akwai abubuwa da dama da ya kamata a yi domin daidaita tunani da yanayin jama'ar yankin, ta yadda za su cire tunanin an maida su saniyar ware a kasar nan."

Ko a makon jiya, Muryar Amurka ta ruwaito ministan na kwadago Chris Ngige, wanda shi ma dan yankin na kudu maso gabas ne, yana bayyana goyon baya ga kiraye-kirayen da yan kabilar Igbo ke yi na mayar da ragamar shugabancin kasar zuwa shiyarsu ya na mai cewa, hakan zai taimaka wajen warware zargin rashin damawa da su.

A yayin amsa tambayoyi a wani shiri mai taken 'News Night' a gidan talabijan na Channels, ya ce ‘yan kabilar Igbo sun dade suna fafutukar ganin ragamar shugabancin ya koma shiyar su lamarin da ya kai ga rarrabuwar kawuna tsakanin al’umman shiyoyin kasar mai mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

A cewar Ngige, lokaci ya yi da za a mara baya ga wadanda ke kiraye-kirayen a mika ragamar mulki ga yan kabilar igbo a zaben shekarar 2023 mai zuwa inda ya yi imanin cewa, idan mulki ya koma kudu, za a magance rikice-rikicen da ke afkuwa a kudu maso gabas da kuma yadda yan shiyyar ke ganin an maida su saniyar ware musamman idan kujera mafi mahimmanci ta farko ta kasance da jagorancin dan kabilar Igbo.

ADAMAWA: Shugabannin al'ummar Igbo dake jihar Adamawa
ADAMAWA: Shugabannin al'ummar Igbo dake jihar Adamawa

‘Yan kabilar ta Igbo sun dade suna kai ruwa rana kan batun cewa, an maida yan yankin saniyar ware, ba a ganin darajarsu a shigo da su a dama da su duk da cewa ba zai iya tantance ko yadda su ke ji na da alaka da farfaganda ne ko akasin haka inda Chris Ngige ya ce, ya amince 100 bisa 100 da fafutukar ‘yan kabilarsa ta Igbo.

A 'yan kwanan nan 'yan kabilar ta Igbo, musamman 'yan kungiyar nan ta fafutukar kafa kasar Biyafara wato IPOB, suka zafafa gwagwarmayar ta su mai dadadden tarihi, ta neman ballewa daga Najeriya, bisa da'awar cewa ana mai da su saniyar ware.

'Yan Kungiyar Fafukar Kafa Kasar Biafra IPOB
'Yan Kungiyar Fafukar Kafa Kasar Biafra IPOB

To sai dai wannan ya janyo babban kalubalen tsaro a yankin, a yayin da 'yan kungiyar suka soma kai hare-hare a kan jami'an tsaro da sauran hukumomin gwamnati, har ma daidaikun jama'ar wasu yankuna musamman 'yan Arewa mazauna yankin.

'Yan sanda da rundunar sojin kasar sun danganta kungiyar ta IPOB da kai hare-haren, a yayin da alokuta da dama kuma jami'an tsaron suke maida martani ta hanyar farmaki kan 'yan kungiyar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG