Kamfanin Twitter ya share wani sashi na kalaman da shugaban Najeriya ]Muhammadu Buhari ya yi ga masu kokarin ta da husuma a kudu maso gabashin Najeriya.
“Da yawa daga cikin wadanda suke rigima a yau, suna yara kanana ballantana su san irin asarar rayuka da aka yi a lokacin yakin basasa. Mu da muka je filin daga muka kwashe wata 30, mun gani.”
Saboda haka, Buhari ya kara da cewa, “za mu bi su ta yadda suke so.”
Buhari ya furta kalaman ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Yakubu Mahmood wanda ya gabatar masa a bayanai kan hare-haren da aka rika kai wa ofisoshin hukumar a sassan Najeriya.
Amma ga dukkan alamu, kamfanin na Twitter ya goge rubutun a ranar Laraba, wanda Muryar Amurka ta yi kokarin lalubo shi a shafin na Twitter, amma abin ya ci tura.
Amma kamfanin na Twitter, ya bar wani sako dake cewa, “wannan sakon ya sabawa ka’idojin da Twitter ya shimfida.”
Sai dai gwamnatin ta Najeriya, ta bakin ministan yada labarai Lai Mohamed, ta zargi kamfanin na Twitter da nuna goyon baya ga kungiyar IPOB wacce hukumomin Najeriyar suka haramta ta.
Karin bayani akan: Twitter, IPOB, INEC, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, Biafra, da Najeriya.
Rahotanni sun ruwaito Mohamed yana zargin Twitter da yin biris da kalaman da shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu yake wallafa a Twitter da shi da magoya bayansa.
“Kungiyar da take ba mambobinta umarnin su kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda, su kashe ‘yan sanda, su kai hari gidan yari, su kashe gandurobobi, sai kuma a ce shugaban kasa ba shi da ikon ya nuna fushinsa? Mohamed ya fadawa manema labarai a Abuja a ranar Laraba, kamar yadda kafafen yada labaran kasar da dama suka ruwaito.
Lai ya kara da cewa, “Twitter na da ka’idojinta, amma ta kwan da sanin cewa, ba ka’idoji ba ne na duniya, duk shugaban kasar da ya ga wani abu da bai kwanta masa a rai ba, yana da ‘yanci ya bayyana ra’ayinsa.”
A ‘yan watannin baya-bayan nan, yankin kudu maso gabashin Najeriya, na fama da hare-haren ‘yan bindiga, wadanda ake dangantawa da kungiyar IPOB da ke fafutukar kafa kasar Biafra, ko da yake, ta sha nesanta kanta da rikice-rikicen.
Mafi akasarin hare-haren akan kai su ne akan ofisoshin ‘yan sanda da jami’an tsaro da kuma na hukumar zabe ta INEC.
An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi