Ganin rashin fahimtar addinai da ke faruwa a cikin al'umma har aka kai ga rasa rayuwan wasu mutane guda biyu, daya a Jihar Sokoto da nan Abuja a watannin baya, da yadda rashin kaunar juna da rarrabuwar kawuna ke ci gaba da faruwa a kasar, shi ne ya sa kungiyar wanzar da zaman lafiya tsakanin addinai wato INTERFAITH DIALOGUE FOR PEACE a turance, ta kaddamar da wani kundi mai dauke da shafuka 20 wanda zai kawo saukin fahimtar wasu bangarori na addinan da ke magana kan zaman lafiya da kaunar juna, da yadda za a yi mu'amala ba tare da tashin hankali ba.
Reberen Joseph John Hayab jami'i ne a cikin wannan kungiyar, ya yi karin haske kan abinda ya sa suka dauki wannan mataki.
Reberen Hayab ya ce sun lura akwai rashin fahimta a bangarorin biyu, kuma sun lura mutum yana so a tunatar da shi a kullum, shi ne ya sa suka dauki shekaru uku suna wannan aiki na tantancewa da zakulo fannonin da ke bayani kan zaman lafiya da kaunar juna a cikin littatafan biyu wato Alqur'ani da Baibul, suka kunshe su a wannan kundi, wanda zai zama da saukin karatu.
Reberen Hayab ya ce ba sai mutum ya nemi bude Baibil ko Alqur'ani a duk lokacin da zai yi karatu ba. Reberen Hayab ya ce sun dauki wannan matakin ne domin magance matsalolin da suka faru a baya, da wadanda ke faruwa a yanzu ko wadanda ake gudun faruwan su a gaba.
Amma ga kwararre a fannin zamantakewar dan Adam Abubakar Aliyu Umar, ya yi nazari cewa yawancin matsalolin da ke faruwa sun taso ne daga Malaman addinan, a inda ya ce sun tashi ne daga bautar Allah zuwa bautar kudi. Abubakar ya ce tunda aka kafa kasa aka kawo wa dan adam ka'idoji na zamantakewa, amma mutane suka butulce wa littattafan addinai.
Abubakar ya ce sai Malamai sun tsarkaka kawunansu da yanayin wa'azinsu tare da nuna alamu na yadda su kansu suke zama da wadanda addinin su ba daya ba, shi ne zai sa mabiya su yi koyi da yanayin zamantakewa mai ma'ana tsakanin juna.
To sai dai daya cikin jami'an wannan kungiyar Lantana Abdullahi Bako ta yi karin haske akan batun cewa an lura rashin fahimta ne da ke faruwa a cikin al'umma tare da bada misali da abinda ya faru a watannin baya a Jihar Sokoto da ma nan Babban Birnin Tarrayya Abuja.
Lantana ta ce za su dauki matakin fadada wurare da za su kai kundin domin ci gaba da wayar da kan al'umma kan muhimmancin bin ka'idojin da ke kundin.
Shi ma Mataimakin Shugaba a wannan kungiya ta wanzar da zaman lafiya tsakanin addinai, Dokta Yakubu Yusuf Arrigasiyyu ya yi karin bayani kan wannan kundi da yadda zai amfani al'umma.
Arrigasiyyu ya ce sun zakulo wadannan ayoyi na muhimman littatafan biyu, da Al'qurani da Baibul ne, saboda magance irin matsalolin da ake fuskanta, kuma suka yi shi cikin bayanai masu sauki da kowa zai iya fahimta, kuma za su yi kokarin danganawa da yan majalisu domin kundin ya samu karbuwa.
Manazarta na ganin wannan kundi ya zo akan gaba domin an samu wani yanayi na rigingimu, da ke da alaka da cin mutunci ko furta kalamai na kyama a bangaren mabiya addinan biyu a baya, da ya kawo zub da jini a wasu sasa na kasar.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna