A lokacin da yake gabatar da sanarwar a gaban daukancin lauyoyin kasar, shugaban kungiyar lauyoyi ta Barreau des Avocats du Niger, Batonnier Kadri Oumarou, ya bayyana irin tarnakin da suke zargin hukumar yaki da cin hanci ta COLDDEF na yi wa ayyukansu, a yunkurin kare wasu jiga-jigan gwamnatin da sojoji suka kifar da ake tuhuma da rub-da ciki akan dukiyar kasa.
Kungiyar na mai tunatar da hukumomin mulkin soja matsayin samun kariya a jerin ‘yancin da dokokin cikin gida da na kasa da kasa suka yi tanadi ga kowane mutun a matsayinsa na dan Adam.
Yunkurin ankarar da shugabanin harkokin shara’a irin illolin da ke tattare da wannan kulli ya ci tura, inji lauyoyin.
Kungiyar na mai mamakin yadda hukumar COLDDEF ke mursisi kan ‘yancin bada kariya, alhali abu ne da hukumomin mulkin soja da kansu suka yi amanna da shi.
Muryar Amurka ta tuntubi kakakin COLDDEF Son Allah Dambaji, domin jin martanin da hukumar za ta mayar, sai dai ya fadi cewa suna shirin gudanar da taro kan wannan batu, a halin yanzu ba zai iya cewa kala ba, saboda haka a jira idan komai ya kammala za a ji daga gare su.
Wannan kace-nace game da tsarin aikin na hukumar da gwamnatin mulkin sojan Nijer ta kafa na wakana ne a wani lokaci da wasu ‘yan kasa ke zarginta da jinkiri wajen tatso kudaden da ake hasashen an wawure a shekarun baya.
Saurari rahoton cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna