NIAMEY, NIGER - Wata sanarwa da aka wallafa a kafafen sada zumunta a ranar Litinin 8 ga watan Janairu 2024, wacce babban akawun kotun hukunta laifukan soja Chef d’escadron Moumouni Abdoulaye ya sakawa hannu ta ce kotun, a zaman da ta yi, ta yi wa Salim Bazoum sakin talala a bisa sharadin amsa kiran alkali mai bincike a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
‘Dan shekaru 23 a duniya, Salim Bazoum ya zo hutun makaranta ne a dai-dai lokacin da sojojin CNSP suka yi juyin mulki, mafari ke nan da aka tsare shi lokaci guda da mahaifansa bisa zarginsa da hada kai wajen yi wa hukuma zagon kasa ko barazana ga hukuma.
Lamarin ya sa an shiga safa da marwa a tsakanin kotuna kafin a ranar Litinin a amince wa bukatar ba da belinsa, abin da wani dan uwansa Chayib Mohamed ya bayyana a matsayin na farin ciki .
Lauyan iyalin shugaba Mohamed Bazoum Me Ould Salem Moustapha wanda bai so ya yi furuci ba saboda dalilan ka’idar aiki, ya tabbatar da hukuncin kotun ta Tribunal Militaire.
Sakin hambararren shugaban kasar Nijer da iyalinsa na daga cikin sharudan da kungiyar ECOWAS ta gindaya wa hukumomin mulkin soja kafin a cire wa kasar takunkumi.
Haka kuma a zamanta na ranar 15 ga watan Disamban 2023, kotun CEDEAO ta umurci mahukuntan wannan kasa su sallami Mohamed Bazoum da iyalinsa.
A cikin gida ma wasu kungiyoyi irinsu FCR sun yi ta gwagwarmaya akan irin wannan bukata, dalili ke nan da shugabanta Souley Oumarou ya bayyana sakin Salim a matsayin wani ci gaba a yunkurin warware wannan dambarwa.
Kasashen Togo da Saliyo ne CEDEAO ta dora wa nauyin shiga tsakani a rikicin siyasar ta Nijar, saboda haka b ada belin Salim Bazoum Mohamed ke da wuya, ministan harkokin wajen Togo Robert Dussey ya fice da shi zuwa kasarsa a cewar wata majiya mai zaman kanta.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna