Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NLC Za Ta Dakatar Da Zanga-zanga Bayan Ganawa Mai Ma’ana Da Tinubu


Lagos, Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)
Lagos, Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)

Kungiyar NLC karkashin jagorancin shugabanta, Comrade Joe Ajaero, da na kungiyar kwadago, Comrade Festus Usifo, sun yi wata ganawa da Tinubu da yammacin jiya Laraba a Abuja a cewar wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu shawara kan sha’anin sadarwa Dele Alake ya fitar.

Kungiyar ta NLC sun zabi ci gaba da hulda mai ma’ana da gwamnati domin warware duk wasu batutuwan da suka shafi aiki da kuma ‘yan Najeriya baki daya

Masu Zanga-zangar Lumana Ta NLC A Jihar Kano
Masu Zanga-zangar Lumana Ta NLC A Jihar Kano

Sakamakon tattaunawa mai ma'ana da Shugaba Tinubu da kuma yakinin da suke da shi na iya karfafa, la'akari ga dukkan batutuwan da kungiyar kwadago ta gabatar, shugabannin Kwadago sun yanke shawarar dakatar da zanga-zangar.

Zanga-zangar NLC a Abuja, babban birnin Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)
Zanga-zangar NLC a Abuja, babban birnin Najeriya (Hoto: Facebook/NLC)


Shugaba Tinubu ya ba da tabbacin sa ga shugabannin Kwadago cewa matatun mai na Fatakwal za su fara aiki a watan Disamba na 2023 bayan kammala kwangilar gyaran da ake yi tsakanin kamfanin NNPC da na kasar Italiya, Maire Tecnimont SpA.

Shugaba Tinubu ya tabbatar wa shugabannin jam’iyyar Labour cewa zai ci gaba da yin aiki don amfanin Nijeriya tare da rokon shugabannin jam’iyyar da su hada kai da shi domin a haifi kasa mai inganci da tattalin arziki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG