Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Duniya Yace Talauci Ya Ragu A Duniya, Amma....


A rahoton da ake fitarwa a duk wata shida, Bankin Duniya ya ce har yanzu akwai matsala akan tattalin arziki da kasashen duniya ke fama da shi.

Rahoton ya ce sai an sa himma sosai kafin a rage talauci yadda ya kamata har al'umma su samu walwala.

A rahoton da bankin duniya ya fitar, yayi nuni da cewa tsakanin shekara ta 2013 da 2015 an sami ragowar matalauta sama da miliyan sittin da takwas a duniya sakamakon matakan da ake dauka na bunkasa tattalin arzikin kasashe, ciki harda Najeriya.

Amma masu nazarin tattalin arziki irinsu Aliyu Shamaki na da bambancin ra’ayi, inda yake cewa kada ‘yan Najeriya su rudi kansu. Yau shekaru 58 da samun ‘yancin kai a Najeriya kuma an sami gogayya da kasashen da Najeriya ta fi, amma yau idan aka yi la’akari za a ga sunyi nisan tazara da Najeriya, a cewarsa.

Ya kuma ce duk da kokarin da gwamnatoci ke yi na yaye talauci a Najeriya, har yazu an gagara samun masana tattalin arzikin kasa da zasu zauna su ba gwamnati shawarar yadda talaka zai fita daga kangi .

Ministan kula da ma’aikatar matasa da wasanni Barista Solomon Dalung yace ba a taba yinkurin yaye talauci irin yadda akeyi a gwamnatin shugaba Buhari ba. Missali, a cewar ministan, a cikin shekaru uku an dauki matasa dubu dari biyar aiki da ake basu dubu talatin duk wata. Na biyu, akwai dan jari da ake ba mata don a tallafa masu wajen yin sana'o'i.

Bayan haka kuma akwai tsarin ba yara ‘yan makaranta abinci don a kara masu kwarin guiwa a cewar ministan.

Bankin duniya ya ce abu ne mai wahala a cimma burin rage matalauta har kashi 3 cikin 100 a shekarar 2030, idan aka duba yadda tattalin arzikin kasashe da dama ke tafiyar hawainiya.

Ga labari cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG