Jam’iyyu masu tsaurin ra’ayin Islama na amfani da shawarar da Amurka ta yanke ta amincewa da Birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isira’ila a matsayin wani abin kafa hujja wajen samo mabiya, al’amarin da ga dukkan alamu za a yi amfani da shi a lokutan yakin neman zaben siyasa, a kasashe masu rinjayen Mussulmi.
Sanarwar da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar ranar Laraba ta haddasa yawan zanga-zanga a wasu kasashen duniya, ta yadda abin ma ya kai ga arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro a yankunan Falasdinawa. Ana kyautata zaton zanga-zangar za ta fi tsanani yau Jumma’a a kasashe irin Indonesia da Turkiyya da Turkiyya a yau Jumma’a.
Mai magana da yawun Fadar Shugaban kasar Afghanistan y ace wannan matakin zai yi illa ga batun samar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya, kuma duk wani abin da za a yi ba da hadin kan Falasdinawa ba, ba zai yi tasiri ba.
A halin da ake ciki kuma jiya Alhamis Fadar Shugaban Amurka ta White House ta musanta cewa sanarwar da Shugaba Trump ya yi ta daga ofishin jakadancin AMurka daga Tel Aviv zuwa Birnin Kudus na nufin gwamnatinsa ta fice daga shirin samar da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.
“Hasali ma, kamar yadda Shugaban kasa ya ce, har yanzu mu na masu bayar da himma ga batun saman da zaman lafiya kamar yadda mu ka saba, kuma mu na so mu cigaba da matsa kaimi wajen gabatar da wannan batu,” a cewar Sakatariyar Yada Labaran Fadar White House Sarah Kuckabee Sanders.
A wata takardar bayanin da Rasha ta fitar, wadda ta zo ma Isira’ila da ba-zata, Rashar ta ce za ta dau Yammacin Birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isira’ila, amma kuma za ta dau Gabashin Birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Falasdinu da za a kafa.
Facebook Forum