Shugaban kasar Amurka Donald Trump yace Amurka ta amince kuma zata fara daukar birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila kuma za ta dauke ofishin jakadancin Amurkan daga Tel Aviv zuwa birnin na Qudus,matakin da ya ke jawo kace-nace a fadin duniya.
"Birnin Qudus ba shine zuciyar addinai guda uku ba, amman yanzu shine zuciyar siyasar da sukayi fice a duniya." Inji Shugaba Trump ya kuma kara da cewa," Fiye da shekaru 70 da suka wuce mutanen Isra'ila sun gina kasar da ko wane iaddini, musulmi, kirista ko yahudu da ma dukannin addinai za su iya addininsu cikin walwala ba tare da wata tsangwama ba."
Trump ya jaddada cewa Amurka zata ci gaba da taimakawa wajen samar da yarjejeniyar zaman lafiya da kwanciyar hannkali a Falasdin da Isra"ila.
"Ina da niyyar yin duk abinda zan iya don ganin an yi wannan yajejeniyar," inji shi.
Kasashen larabawa da na musulmai sun yi gargadi akan wannan matakin domin a ganinsu zai ingiza tashe-tashen hankula a yankin kuma zai ya kawar da kokarin da Amurka ke yi na gann ta kawo zaman lafiya a tsakanin Isra'ila da Falasdin
Falasdinawa sun yi kiran zanga-zangar baccin rai na kwana uku don nuna rashin amincewarsu da wannan matakin da Donald Trump ya dauka.
Facebook Forum