Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sauran Kasashen Duniya Zasu Bi Sahun Amurka Akan Birnin Qudus -Netanyahu


Benjamin Netanyahu, Frayim Ministan Israila
Benjamin Netanyahu, Frayim Ministan Israila

Bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya fito karara jiya Laraba ya bayyana amincewar kasarsa da birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar Israila abun da gwamnatocin baya na Amurka suka guje ma yi da sauran kasashen duniya, yau Firayim Ministan Israila yayi amanna sauran kasashen duniya zasu bi sahun Amurka

A yau Alhamis Firaiministan Isra’ial Benjamin Netanyahu, ya ce ba ya tantama, sauran kasashen duniya ma za su bi sahun Amurka wajen ayyana Kudus a Matsayin babban Birnin Isra’ila.

Ya kara da cewa, da zaran Amurka ta maida ofishin Jakadancinta zuwa Birnin, sauran kasashen duniya ma za su kwaikwayeta.

A jiya Laraba shugaba Trump ya ayyana Kudus a matsayin babban Birnin na Isra’ila inda y ace:

“Na yanke shawarar cewa, lokaci ya yi da za a ayyana Birnin na Kudus a matsayin babban Birnin Isra’ila a hukumance, duk da cewa, sauran gwamnatoci sun yi alkawarin yin hakan a lokacin yakin neman zabensu, sun gaza cika alkawarinsu. Amma ni a yau zan aiwatar da hakan.”

Firai ministan Isra’ila ya ce, gwamnatinsa na kan tuntubar sauran kasashen, ba ta tare da ya ambaci sunan wata kasa ba, yayin da yake wani jawabi a ma’aiktar harkokin wajen Isra’ila.

Rudnunar sojin Isra’ila ta sanar da shirin tura karin dakarunta a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, a wani mataki da ta kira, “zaman shirin yiwuwar samun wani ci gaba.”

Wannan matsaya da Trump ya dauka ta sauya akalar shirin Amurka akan Kudus, ya janyo kakkausan suka daga shugabannin Falasdinawa, inda shugaba Mahmoud Abbas ya ce wannan matsaya ta Trump daidai take da janyewar Amurka a matsayinta na mai shiga tsakani domin sasanta rikicin yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG