Kungiyar hadin kan Afrika ta sassauto daga matsayinta dangane da gwamnatin rikon kwaryar kasar Libya jiya Laraba, sai dai har yanzu bata bayyana amincewa da halalcin shugabancin kungiyar wucin gadin ba.
A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar bayan wani taro a Afrika ta kudu, kwamitin kungiyar AU da aka kafa kan batun kasar Libya ya bayyana niyar aiki tare da majalisar wucin gadin da sauran mutanen kasar Libya wajen kafa gwamnatin hadin kan kasa.
Kawo yanzu kungiyar hadin kan Afrika tayi watsi da kiraye kirayen da ake yi na amincewa da majalisar wucin gadi a maimakon haka ta bayyana bin mataki na dabam na kafa gwamnati a kasar Libya.
Jiya Laraba kungiyar ta bayyana yin na’am da himmar majalisar wucin gadin na ganin hadin kan kasa, da cewa tana goyon bayan burin majalisar na hada kan dukan ‘yan kasar Libya domin gina kasa ba tare da nuna banbanci ba.
Kwamitin Kungiyar hadin kan Afrikan ya kuma bayyana shirin aiki tare da sauran shugabannin yankin da cibiyoyin kasa da kasa wajen kafa gwamnati cikin kwanciyar hankali da lumana a kasar Libya.