‘Yan sandan kasa da kasa na Interpol sun bayar da sammacin kama tsohon shugaban Libiya Muammar Gaddafi bisa zargin aikata manyan laifuka na cin zarafin bil’adama.
A wata sanarwar da suka bayar a yau Jumma’a, ‘yan sandan na Interpol sun ce sun bayar da kwakkwaran sammacin kama Mr. Gaddafi, da dansa Saif al-Islam da wani tsohon shugaban hukumar leken asiri Abdullah al-Senussi, tare da kiran dukkannin kasashe 188 da ke ma’amala da Interpol din su taimaka wajen ganowa da kuma damke su.
Sakatare-Janar din Interpol Ronald Noble ya bayyana Mr. Gaddafi da cewa mai gudun kamu ne, y ace sammacin kama shin zai taimaka wajen takaita ketara kan iyakokin kasashen da ya kan iya.
Gaddafi, wanda har yanzu ba a san inda yak e ba, ya cigaba da boyewa tun bayan da dakarun da ke adawa da gwamnatin su ka abka cikin Tripoli, babban birnin ran 21 ga watan Agusta.
A jiya Alhamis, wani gidan talabijin din Syria ya saka muryar da aka ce ta Gaddafi ce, inda ya karyata rahotannin cewa watakila ya tsere daga kasar zuwa Janhuriyar Nijar das u ke makwabtaka. Mr Gaddafi ya ce har yanzu dakarunsa za su iya tinkarar dakarun Majalisar Shugabancin Wuccin Gadin, day a bayyanasu da cewa beraye ne, kwari kuma bata gari.