Gwamnatin kasar jamahuriyar Nijer na neman a taimaka ma ta, ta kula da kan iyakokin ta da kasar Libiya a daidai lokacin da wasu tsoffin jami’an hambararriyar gwamnatin kasar Libiya ke tserewa su na shiga kudancin kasar Nijer.
Ministan shara’ar kasar jamahuriyar Nijer, Morou Amadou ya ce kasar shi na bukatar matakan tabbatar da tsaro da sa ido ta jiragen sama da kuma managartun matakan tattara bayanan leken asirin da za su iya taimaka ma ta, ta kula da yankin hamadar da ke da fadin mita miliyan shidda murraba’i a kan iyakar ta da Libiya.
Ya ce kudaden da ake kashewa wajen kara yawan jami’an tsaro masu sintiri a kan iyakar arewacin kasar ne ke hana yin ayyukan raya yankin.
Tsadar tabbatar da tsaron kan iyaka nauyi ne babba ga matalauciyar kasa kamar jamahuriyar Nijer wadda ke fama da matsalolin karancin abinci akai-akai.
Jami’an tsohuwar gwamnatin kasar Libiya da su ka tallaka kan iyaka su ka shiga kasar jamahuriyar Nijer sun hada da wasu tsoffin janar-janar din soji su biyu, da shugaban rundunar jami’an tsaron hambararren shugaban kasar Moammar Ghadafi da kuma dan shugaba Ghadafi daya.
Yanzu haka dan shugaba Ghadafin mai suna Saadi, da ke kasar Nijer, ya na zaune a cikin wani yanayi mai kama da zaman daurin talala a Niamey babban birnin kasar.
Morou Amadou ya ce tun ma kafin a fara yakin kasar Libiya, Nijer ta na fama da matsalar kan iyaka saboda 'yan ta'adda masu alaka da al-Qaida.
Kungiyar al-Qaidar yankin kasashen Musulmin arewacin Afirka na gudanar da ayyukan ta a duk fadin yankin Sahel wanda wani zirin kasa ne da ke tsakanin hamadar Sahara da sauran nahiyar Afirka. Kungiyar ta sha aikata sace-sacen mutane da kashe-kashen kai a Mauritania da Aljeriya da Mali da kuma jamahuriyar Nijer.