Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An rutsa dan Moammar a Niger

Saadi Gadhafi, dan tsohon shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi (File Photo)
Saadi Gadhafi, dan tsohon shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi (File Photo)

Gwamnatin Niger tace wata rundunar sojojin kasar da ke sintiri ta tsaida ayarin motoci dake dauke da dan hambararren shugaban kasar Libya Moammar Gadhafi, da wadansu mutane tara bayan sun tsallaka hamada daga Libya suka shiga kasar.

Ministan shari’a Marou Ahamadou yace dan Mr. Gadhafi ya shiga kasar Nijar ba tare da izini ba kuma dakarun kasar dake sintiri kan iyakar hamadar tsakanin Niger da Libya suka kama shi.

Yace sojojin Nijar sun raka kwanban motocin zuwa birnin Agadez. Ya gayawa manema labarai cewa yana sa zuciya za a tasa keyar Libiyawan zuwa Niamey babban birnin kasar yau litinin ko gobe Talata.

Da aka tambayeshi ko an tsare Sa’adi Gadhafi yace Nijar zata cika hakkinta na jinkai.

Cikin makon jiya ne Nijar ta kyale tsohon babban jami’in tsaron Libya ya shiga kasar a wani mataki da ta kira na jinkai. An bada takardar sammaci a kan Moammar Gadhafi da kuma danshi Saif al-Islam amma banda Saadi Gadhafi wanda a watan jiya ya yi kokarin tattaunawa domin kawo karshen fadan da majalisar wucin gadi. Sai dai dan’uwanshi ya yi watsi da wannan yunkurin ya lashi takobin ci gaba da yaki.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa wa’adin tattaunawa domin yin sarandar biranen kasar Libya uku dake karkashin ikon dakarunn dake goyon bayan Gadhafi ya wuce.

Kawo yanzu babu tabbacin inda tsohon shugaban kasar Libyan yake.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG