Alhamis shugabannin Ingila da Faransa suka kai ziyara a biranen Libya biyu da ba a juma da ‘yanta su ba, a dai dai lokacin da sojojin sabuwar gwamnatin wucin gadin kasar suka yi yunurin kai farmaki kan mahaifar Gadhafi a Sirte.
Dubban ‘yan kasar Libya ne da suke sowa suka marabci PM Ingila David Cameroon da kuma takwaransa na Faransa Nicolas Sarkozy, a babban birnin kasar Tripoli da kuma Bengazi dake gabashin kasar inda daga nan ne aka fara bore kan gwamnatin Gadhafi.
Shugabannin biyu sun fada cewa yau jumma’a zasu gabatar da wani daftarin ga MDD da zai bukaci a kafa ofishin majaisar a Libya, janye takunkumi da aka azawa kadarorin kasar, da kuma kawar da dokar hana shawagin jiragen farar hula, da kuma hanin sayarwa kasar makamai.
Sun yi alkawarin zasu tallafawa sabuwar gwamnatin kasar wajen ganin ta shimfida iko a duk fadin kasar, da kuma gano duk inda tsohon shugaban kasar da wakilan gwamnatinsa na kusa da kusa suke. Haka kuma Mr. Cameroon da Mr. Sarkozy sun yi alkawarin kungiyar NATO zata ci gaba da daukan matakan soji a kasar muddin akwai bukatar haka.
A cikin wunin jiya Alhamis din ne kuma a wani mataki na ba zata sojojijn ‘yan tawayen Libya suka fasa shingen tsaro da magoya bayan Gadhafi suka kafa suka shiga birnin Sirte, mai tazarar kilomitan 450 daga birnin Tripoli.
Dubban mayakan ‘yan tawaye daga Misrata ne suka shiga tsakiyar birnin, inda suka fuskanci tirjewa mai tsanani daga magoya bayan Gadhafi.