Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mali Na Jimamin Rasuwar Tsohon Shugaban Kasa Ibrahim Boubacar Keita


Tsohon Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita.
Tsohon Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita.

Tsohon shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita wanda aka fi sani da sunan IBK ya rasu. Ya rasu yana da shekaru 76.

Sojojin kasar sun hambarar da Keita kusan shekaru biyu da suka gabata.

Ya hau kan karagar mulki a watan Satumban 2013 kuma an sake zaben shi a wa'adi na biyu na shekaru biyar a shekarar 2018.

A lokacin shugabancinsa ne 'yan tawaye masu kishin Islama suka mamaye yankuna da dama na kasar ciki har da tsohon birnin Timbuktu.

A shekara ta 2020, dubbun-dubatar 'yan kasar Mali suka fito kan titunan babban birnin kasar Bamako domin neman ya yi murabus.

Mutuwar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin gwamnatin mulkin sojan Mali da kuma kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, wadanda suka kakaba wa kasar sabbin takunkumi.

Har ila yau kasar ta Mali na cikin takun saka tsakaninta da Faransa kan matakin da ta dauka na tura sojojin haya na Rasha da ake kira Wagner Group zuwa kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG