Kungiyar direbobin tanka masu dakon man fetur a Najeriya ta dakatar shirin ta na tsunduma yajin aiki.
Babbar kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta kasa wato NUPENG, wadda kungiyar direbobin tankar ke karkashin ta, ita ce ta ba da sanarwar dakatar da yajin aikin da aka shirya somawa a yau Litinin.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya ruwaito shugaban kungiyar ta NUPENG a shiyyar kudu maso yamma, Tayo Aboyeji, yana cewa an janye yajin aikin ne sakamakon sa baki da gwamnatin tarayya ta yi.
Aboyeji ya ce kungiyar ta direbobin tanka ta aminta da dakatar da shiga yajin aiki, domin ba da dama ga wakilanta da na gwamnatin tarayya, tattaunawa da samo hanyoyin magance matsalolin da suka taso.
Tuni kuma aka soma tattaunawar tsakanin bangarorin biyu akan lamarin, inda aka ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta yi alkawarin yin duba da idon rahama kan korafe-korafen dirobobin jigilar man fetur din.
A ranar Assabar da ta gabata ne dai kungiyar ta NUPENG ta ba da sanarwar cewa direbobin tanka masu jigilar man fetur za su soma yajin aiki a yau Litinin, sakamakon mawuyacin halin da titunan kasar suke ciki, da kuma wasu korafe-korafe.
Aboyeji ya ce kungiyar ta yi asarar rayukan membobin ta da dama da kuma dukiyoyi, sakamakon lalacewar tituna, inda kuma ya yi korafi kan yadda direbobin ke kwashe tsawon kwanaki 5 zuwa 6 kafin su isa Abuja daga Legas.
To sai dai kwana daya da ba da sanarwar yajin aikin, kamfanin man fetur na kasar wato NNPC, ya roki direbobin da su mayar da wukar su kube kan shiga yajin aikin, domin kaucewa jefa ‘yan Najeriya a cikin ukuba.
Wata sanarwa da babban daraktan sashen hulda da jama’a na kamfanin Garba Deen Muhammad ya fitar, ta ce duk da yake aikin shimfida tituna ba hakki ne da ya rataya kan kamfanin na NNPC ba, to amma duk wani abu da zai kawo cikas ga jigilar albarkatun man fetur da rarraba su a sassa daban-daban na Najeriya, zai taba aikin kamfanin, ya kuma jefa ‘yan kasar a cikin ukuba.
To sai dai duk da haka kamfanin na NNPC ya bai wa direbobin tabbacin cewa zai fito da wasu tsare-tsare da za su gaggauta samar da maslaha kan matsalolin rashin kyawun tituna, domin karfafawa kokarin da hukumomin gwamnati ke yi na magance wannan matsala.