Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar al-Shabaab Ta Somaliya Ta Kashe Mutane Bakwai 


Mayakan Al-Shabab
Mayakan Al-Shabab

Ma'aikatar yada labaran Somaliya da kungiyar masu fafutuka sun ce mayakan al Shabaab masu da’awar kishin Islama sun kashe sojoji akalla bakwai a wani sansanin sojin kasar a yau Jumma’a, a wani gari da gwamnatin kasar ta sake kwacewa.

WASHINGTON, D.C. - Daga karshe dai an dakile harin, kamar yadda wani jami'i a sansanin da ke garin Galcad da ke tsakiyar kasar Somaliya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Ya ce wadanda suka mutu sun hada da mataimakin kwamandan sansanin, wanda ke cikin rundunar da Amurka ta horas da su da ke can.

Mayakan Al-Shabab
Mayakan Al-Shabab

Harin dai ya nuna irin mummunar barazanar da kungiyar al-Shabaab ke yi wa sojojin kasar Somaliya, ko da bayan harin da gwamnatin kasar ta kaddamar a shekarar da ta gabata ya samu gagarumar nasara kan mayakan da ke da alaka da al-Qaeda.

Kaftin Issa Abdullahi ya ce mayakan Al Shabaab sun kai hari a sansanin na Galcad da sanyin safiyar yau Juma'a, inda suka tayar da bama-bamai da motoci tare da harba makamansu.

Rundunar ta Danab ce ke tafiyar da sansanin, wani rukunin kwamandojin da Amurka ta horas da su, wadanda suka shiga farmakin da ake kai wa mayakan.

Mayakan Al-Shabab
Mayakan Al-Shabab

Ma'aikatar yada labaran Somaliya, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce baya ga al-Shabaab da ta kashe sojoji bakwai, sojojinsu sun kashe mayakan kungiyar 100 tare da lalata motocin daukar bindigogi biyar.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta al Shabaab ta fitar ta ce ta hanyar mu'ujiza ta mamaye sojojin da Amurka ta horas da su a garin tare da kashe sojoji da dama.

Dama gwamnatin kasar da al-Shabaab sukan saba kan adadin da su ke bayarwa na wadanda suka mutu a hari guda.

Tun a shekara ta 2006 ne kungiyar ke fafutuka don hambarar da gwamnatin kasar tare da kafa nata tsarin mulki, bisa tafarkin Musulunci a cewarta.

-Reuters

XS
SM
MD
LG