Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar al-Shabab Ta Tilastawa Kananan Yara Dubu Biyar Aikin Soji A Somaliya


Wani babban jami’in majalisar dinkin duniya mai kula da asusun kula da kananan yara na duniya ya bayyana cewa akwai kiyasin kananan yara dubu biyar (5000) da kungiyar al’shabab ta tilastawa yin ayyukan soji a Somaliya a yayin da kungiyar ke ci gaba da neman yada ra’ayoyin ta a yankin.

A wata hira da muryar Amurka sashen Somaliyanci, babbar shugabar asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya Susannah Price, ta bayyana cewa an bada rahoton karuwar adadin amfani da kananan yara a ayyukan soji.

Jami’ar ta kara da cewa “wannan abin damuwa ne kwarai, kuma mun san cewa akwai kananan yara kusan dubu hansin da kungiyar al-shabab take kamawa tana horas dasu ta hanayar yaudarar su da kuma yin amfani karfi da yaji domin gudanar da ayyukan saja a yunkurin da kungiyar ke yi na fadada ayyukan ta”.

“Wasu lokuta suna basu kudi, ko abinci, wannan ya nuna cewar ‘yan kungiyar na auna kananan yaran dake zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira ne domin cimma burin su”.

Hukumar UNICEF ta bada rahoton cewa a shekarun da suka gabata an bada kiyasin kananan yara tsakanin dubu biyu zuwa dubu uku, wadanda suka kama daga shekaru tara da haihuwa shiga aikin sojan kasar ta Somali.

Ta yi wannan jawabi ne a yayin da ake cigaba da gudanar da bukin ranar yaran Afirka ta duniya mai taken “Kare Hakkin Yara Daga Rigingimu Da Tashin Hankula A Nahiyar Afirka”.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG