Yawan rubutun da ake yi a shafin sadarwa na Facebook na yin kasa, a cewar ‘daya daga cikin shugabannin kamfanin, kuma wadda ke ganin nan gaba shafin zai kasance na hotunan bidiyo ne kadai.
Mataimakiyar shugaban kamfanin ta nahiyar Turai da Gabas ta Tsakiya da kuma Afirka, Nicola Mendelsohn, tace yawan hotunan bidiyo a Facebook na kara yawa cikin gaggawa.
Yanzu haka dai ana kallon hotunan bidiyo har sau Biliyan 8 a rana, wanda hakan ya karu ne daga Biliyan 1 a shekarar da ta gabata.
A baya dai shugaban Facebook Mark Zuckerberg, yayi ta magana kan muhimmancin da hotan bidiyo ke da shi a shafin Facebook, sai gashi Nicola ta dauki wannan batu zuwa matakin gaba, har ma tana harsashen hakan zai iya kawo karshen yin rubutu a shafin na Facebook.
Kamar yadda take cewa, hotan bidiyo shine hanya mai sauki da mutane zasu iya bayyana sakonsu ga duniya.