Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Abubuwa Da Mutun Kanyi A Cikin Bacci Batare Da Ya Sani Ba!


Wasu abubuwa bakwai 7, da mafi akasarin mutane kanyi a lokacin da suke bacci. Bincike ya nuna cewar, sau da yawa idan mutane suna bacci, su kanyi wadannan abubuwan batare da sun sani ba. A wasu dare da yawa, bacci wani ni’ima ne da yake taimakama jikin mutun, wajen ginuwa da samun lafiya.

Da yawa idan mutun yayi tunanin abu da yake sha’awa ko yake tsoro da rana, da’akwai alamun mutun zai iyayin mafarkin wannan abun. Haka sau da dama mutun kanji a cikin baccin shi, kamar zai fado daga wani tudu. Wani lokaci mutun kan farka daga bacci, amma yaji wani bangaren jikin shi baya aiki yadda ya kamata, to a wannan lokacin yana da kyau mutun kada ya tashi daga kan gado sai ya dan natsa.

A dai-dai wannan lokacin kwakwalwar mutun tana bukatar daidaita kanta, kamin ta aika ma sauran jikin da jini don gudanar da aikin su yadda ya kamata. Haka ma wasu kanyi magagagin bacci, da har sukan yi tafiya mai nisa duk cikin bacci, sai wasu da kanyi magana suna cikin bacci, kodai akan abun da ya faru da rana kokuma wasu sanbatu da basu da kai.

Haka idan mutun ya tashi daga bacci, batare da ya samu wani lokaci don natsawa ba kamin ya tashi ya fara wasu abubuwa, hakan yana sama mutun matsanancin ciwon kai, da yake da illa, ba kawai ga kan mutun ba, har ma da sauran sassan jiki, hakan dai na nuni da bukatar da ake da ita, ta natsuwa na kamar minti biyu zuwa ukku kamun tashi daga makwanci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG