Shugaban Kudancin Sudan yace sam, ba ya da niyyar tura sojojinsa don suje suyi yaki da bangaren Arewanci akan batun mallakar yankin nan mai arzikin man fetur na Abyei.
Tun ranar Assabar da ta gabata, sojan arewanci suka kwace wannan yanki kuma har shugaban Sudan, Omar al-Bashir yace yankin zai ci gaba da zama a hannun sashen arewanci ne. Shugaban Kudancin Sudan din, Salva Kiir ya nemi shugaba Bashir da ya janye sojansa daga yankin, amma yace shi baya da niyyar sake komawa fagen yaki da arewanci.
Shugaba Kiir ya jadadda cewa yankin nasa zai kaddamarda cikkaken ‘yancin kansa ran 9 ga watan Yuli na wannan shekara, ko Arewanci na so, ko basa so.
A shekarar 2005 ne dai yakin da sassan biyu suka share shekaru 21 suna gwabzawa, ya kare, kuma, koda yake duka sassan biyu sun aminta da ‘yancin da Kudanci zai samu, suna ci gaba da samun sabanin ra’ayi kan maganar wannan yankin na Abyei wanda ya raba kan iyakarsu.