Rasha ta bayyana sha’awar zama mai shiga tsagani a shawarwarin neman shugaban Libya Moammar Gadhafi yayi murabus,sai dai ba zata bashi mafakar siyasa ba.
Da yake magana a taron kolin kasashe masu arzikin msana’ntu da ake kira G-8 a Faransa,shugaban Rasha Dmitri Medvedev, yayi kira ga Mr.Gadhafi yayi murabus,kuma watakil a sami kasashe da zasu bashi mafaka. Shugaban Rasha ya bayyana cewa,kasarsa zata tura jakada na musamman zuwa tungar ‘yan tawaye a Bengazi,jumma’a.
Tunda farko,mukaddashin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov,yace shugaban na Libya,ya bata duk wani dama da yake dashi, saboda haka ya zama tilas a sami wata hanyar taimaka masa ya sauka daga mulki. A baya, Rasha ta gabatar niyyar shiga tsakani da nufin sulhu tsakanin ‘yan tawaye da bangaren Gadhafi.
Ahalin yanzu kuma,sojoji dake biyayya ga Gadhafi sun sabunta kokarin sake kame birnin Misrata dake hanun ‘yan tawaye.Birni na uku a girma cikin kasar.
Kamfanin dillancin labarai Reuters,yace ana gwabza kazamin fada tsakanin sojojin gwamnati dana ‘yan tawaye ta yammacin birnin. A wani gefe kuma,kamfanin dillancin labaran Faransa,ya ambaci wani babban hafsan NATO,leftanal janar Charles Bouchard,yana cewa sojoji dake biyayya ga Gadhafi sun binne nakiyoyi a a kewayen birnin.
Haka kuma an bada labarin jin manyan fashe fashe a babban birnin kasar Triopoli,a can cikin daren jiya Alhamis.Wasu fashe fashen sun auku ne kusa da gidan shugaba Gadhafi.Sai dai ba a bayyana abubuawa da NATOn take aunawa a hare hare da take aikawa ba nan da nan.