Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata kungiyar kasa da kasa tace za'a yi kisan kare dangi a yankin Abyei na Sudan


Mutane da suka yi hasarar gidajensu ne ke zaune karkashin bishiya, kimamin kilomita dari da talatin daga Abyei.
Mutane da suka yi hasarar gidajensu ne ke zaune karkashin bishiya, kimamin kilomita dari da talatin daga Abyei.

Wata kungiyar kasa da kasa da cewa The satelite sentinel project da turanci, tace akwai yiwuwar za'a kisan kare dangi a yankin Abyei na Sudan

Wata kungiyar nazari ta kasa da kasa da ake cewa The Satelite Sentinel project da turanci, tace akwai alamun ana kokokarin gudanar da kisan kare dangi a yankin Abyei. A makon jiya sojojin arewacin Sudan suka mamaye yankin, matakin daya sa sojojin kudanci suka janye kuma dubban mazauna yankin suka arce.

Kungiyar Satelite Sentinel tace sojojin arewacin kasar da yan yakin sa kai sun lalata sulusi guda na harkokin fara hula a baban birnin Abyei. Wannan kungiya wadda take nazarin yadda al’amurra suke a Sudan, ta hanyar amfani da watan dan Adam, ta kuma tabbatar da rahoto da aka bayar na lalata gada dake kusa da birnin da kuma sace kayayyakin abinci daga masa’antar da shirin samar da wadatar abinci ke adana kayayyakin abinci.

XS
SM
MD
LG