Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Tabbatar Da Hyacinth Alia A Matsayin Gwamnan Jihar Binuwai


HYACINTH ALIA
HYACINTH ALIA

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Binuwai da ke zamanta a Makurdi ta tabbatar da gwamnan Jihar, Hyacinth Alia na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen Gwamanan Jihar. 

Kotun ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna, Titus Uba, suka shigar inda suke kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ta kori karar bisa dalilin cewa kotun bata da hurumin sauraron batutuwan da aka gabatar mata.

Mai shari’a Ibrahim Karaye, ya bayyana cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar saboda batun da aka gabatar a gaban kotun batutuwa ne da suka shafi gabanin zabe kamar yadda sashe na 285 na dokar zabe ya tanadar.

Abubuwan da Mista Titus ke zargin Mista Alia sun hada da batun takardar shaidar karatu na jabu a lokacin tsayawa takara, sai dai kotun ta ce wannan hurumin ba nata bane na hukumar zabe ne wato INEC.

Sakamakon da INEC ta bayyana bayan zaben a watan Maris, Alia ya samu kuri’u 473,933 a gaban babban abokin hamayyarsa Uba na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 223,913.

~YUSUF AMINU YUSUF

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG