PLATEAU, NIGERIA - Jami’iyyar APC da dan takararta na gwamna, Nentawe Yilwatda sun shigar da karar zaben gwamnan ne kan hujjoji uku da suka hada da cewa jami’iyyar PDP bata da zababbun shugabanni kafin lokacin zabe, aringizon kuri’u da kuma cewa Caleb Mutfwang bai da yawan kuri’u da ya kamata a ayyana shi a matsayin gwamna.
Tuni da jami’iyyar ta PDP ta bayyana farin cikinta kan nasarar, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na PDP a Jahar Filato, John Akans ya shaida cewa kotu tayi adalci.
A gefe guda kuwa, jami’iyyar APC a jihar Filato ta ce za ta daukaka kara a kotu ta gaba.
Kakakin jami’iyyar APC a jihar Filato, Sylvanus Namang ya ce ba su yarda da hukuncin na kotu ba saboda kotun ba ta duba hujjojin da suka kai kara a kansu kamar yadda ya dace ba.
A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yan sanda a jihar Filato ta ja kunnen wadanda ke tunanin ta da hankalin jama’a, sakamakon hukuncin, da su sake lale.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Okoro Alawari a wata sanarwa da sanya hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, Alfred Alabo, ya ce rundunar za ta ci gaba da aikinta na tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu.
To sai dai duk da wannan gargadin, jama’a da dama sun fantsama cikin gari da murna da wake-wake kan nasarar zaben.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Dandalin Mu Tattauna