Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Kori Karar PDP Kan Nasarar Gwamna Sule


Gwamnan Jihar Nassara Abdullahi Sule
Gwamnan Jihar Nassara Abdullahi Sule

Kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar PDP, David Umbugadu ya shigar kan nasarar gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a yau Juma’ah.

A cikin hukuncin da kotun koli, mai tawagar alkalai 5, ta yanke ta kori karar kalubalantar nasarar Abdullahi Sule a zaben ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023, bisa rashin cancanta kuma ba ta ci tara ko ba da umarnin biyan kowa diyya ba.

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Abdullahi Sule A Matsayin Gwamnan Jihar Nassara
Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Abdullahi Sule A Matsayin Gwamnan Jihar Nassara

Idan ana iya tunawa a ranar 2 ga watan Oktobar shekarar 2023 ne kotun sauraron kararrakin zabe da ke da zamanta a birnin Lafia ta soke nasarar gwamna Abdullahi Sule tare da bayyana David Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben na watan Maris.

Daga bisani Gwamna Sule da jam’iyyarsa ta APC suka kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara.

A nata bangare, kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke a ranar 23 ga watan Nuwambar shekarar 2023, ta soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben tare da tabbatar da zaben Abdullahi Sule a matsayin gwamna.

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Abdullahi Sule A Matsayin Gwamnan Jihar Nassara
Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Abdullahi Sule A Matsayin Gwamnan Jihar Nassara

Kotun daukaka kara ta tabbatar da cewa kotun ta dogara da hujjojin da ba su yarda da doka ba wajen bayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga Maris.

A cewar kotun daukaka kara, kotun sauraron kararrakin zaben ta yi kuskuren dogaro da hujjoji takwas da ba za’a iya shigarwa cikin kotun ba har ya kai ga ayyana Ombugadu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Abdullahi Sule A Matsayin Gwamnan Jihar Nassara
Kotun Koli Ta Tabbatar Da Zaben Abdullahi Sule A Matsayin Gwamnan Jihar Nassara

A baya dai, kotun daukaka ta kara da cewa sashe na 285, sakin sashe na 5 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999, wadda aka yi wa gyaran fuska; da sashe na 132 sakin sashe na 7 na dokar zaɓe na shekarar 2022 da sashe na 4 sakin sashe na 5 da 6 da kuma sashe na 14 sakin sashe na 2 na jadawalin farko na Dokar Zaɓe; ya bayyana cewa duk wata rubutacciyar takardar rantsuwa dole ne a gabatar da ita tare da takardar korafi, a cikin lokacin da doka ta tanada.

A bisa rashin gamsuwa da hukuncin daukaka kara ne dan takarar PDP, Ombugadu ya garzaya zuwa kotun koli, yana neman ta soke hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG