Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Haramtawa Gwamnoni Rusa Shugabanin Kananan Hukumomi


Kotun Kolin Najeriya
Kotun Kolin Najeriya

A hukuncin da ta zartar a yau Alhamis, Kotun Kolin tace, yin haka na iya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Kotun Koli ta haramtawa gwamnoni rushe majalisun kananan hukumomi da aka zaba ta hanyar dimokiradiya a fadin Najeriya.

A hukuncin da ta zartar a yau Alhamis, Kotun Kolin tace, yin haka na iya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

A karar da Antoni Janar na tarayya ya shigar, gwamnatin tarayya ta bukaci iznin kotun da zai hana gwamnoni yin gaban kansu wajen ruguje majalisun kananan hukumomin da aka zaba ta tsarin dimokiradiya.

Karar ta Antoni Janar din ya shigar nada hujjoji 27.

Wadanda ake kara, gwamnonin jihohin Najeriya 36, sun kalubalanci antoni janar din akan shigar da karar.

Haka kuma, kotun kolin ta baiwa kananan hukumomin kasar 774 ‘yancin cin gashin kai akan gudanar da kudadensu.

A hukuncin da Mai Shari’a Emmanuel Agim ya zartar, Kotun Kolin ta caccaki gwamnonin game da tsawon lokacin da suka shafe suna tauyewa kananan hukumomin ‘yancin cin gashin kai.

Mai Shari’a Agim ya kara da cewar kamata yayi kananan hukumomin kasar nan 774 su rika sarrafa kudadensu da kansu.

Alkalin ya kuma yi watsi da korafe-korafen da gwamnonin da ake kara suka shigar tunda fari.

Kotun Kolin ta bada umarcin cewa da ga yanzu a rika aika kason kudaden kananan hukumomin dake tahowa daga asusun tarayya garesu kai tsaye, a maimakon asusun gwamnatocin jihohi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG