Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Najeriya Ta Haramtawa Gwamnoni Rike Kudin Kananan Hukumomi


Kotun Kolin Najeriya ta haramta wa gwamnonin jihohi rike kudin kananan hukumomi ta na mai cewa ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

A hukuncin da Mai Shari’a Emmanuel Agim ya zartar, Kotun Kolin ta caccaki gwamnonin game da tsawon lokacin da suka shafe suna tauyewa kananan hukumomin ‘yancin cin gashin kai.

Mai Shari’a Agim ya kara da cewa kamata yayi kananan hukumomin kasar nan 774 su rika sarrafa kudadensu da kansu.

Alkalin ya kuma yi watsi da korafe-korafen da gwamnonin da ake kara suka shigar tunda fari.

Kotun kolin ta bada umarcin cewar daga yanzu a rika aika kason kudaden kananan hukumomin dake tahowa daga asusun tarayya garesu kai tsaye, a maimakon asusun gwamnatocin jihohi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG