Wa’adin wakilcin su zai kare ne ranar 10 Maris, 2025, akafin aka kara shi har zuwa 30 Maris, 2026. Gwamnatin Kamaru tace wannan umurni ne na shugaban kasa wanda ya dace da yawan matsaloli da kasar ke fuskanta a wasu yankunan kamar yadda takardar da aka shigar gaban 'yan Majalisar domin nazari ke cewa.
Ba wannan ne karon farko da Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ke daukan matakin tsawaita wa'adin aikin 'yan Majalisa da na Kananan hukumomi. Wasu 'yan siyasa sun bayyana cewa, yin hakan na daya daga cikin abubuwan da shugaban kasa zai iya aiwatarwa kai tsaye.
A bangare guda kuma 'yan jam’iyun adawa musamman na MRC sun kalubalanci wannan matakin da cewa, Shugaban kasar ya yi hakan ne da nufin hana su tsayawa takarar zaben shugaban kasa na watan Oktoba 2025.
Hukumar zaben kasar mai zaman kanta ELECAM ta tsayar da watan Fabrairun shekarar 2025 domin zaben 'yan Majalisar dokoki da na kansiloli bayan haka kuma za a gudanar da zaban shugaban kasa a watan Oktoba 2025. Yanzu dole ELECAM ta sake lale.
Saurari cikakken rahoton Mohammed Ladan:
Dandalin Mu Tattauna