Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Umarci Sadiya Umar Ta Bayyana Yadda Ta Kashe Naira Biliyan 729


Tsohuwar Ministar Jinkai, Sadiya Umar Farouk
Tsohuwar Ministar Jinkai, Sadiya Umar Farouk

Babbar Kotun Jihar Legas ta umarci tsohuwar Ministar Jinkai da walwalar jama’a Sadiya Umar Faruk, ta bayyana yadda ma’aikatar ta, ta kashe Naira Biliyan 729 karkashin kulawar ta, bayan da kungiyar kare 'yancin 'yan kasa da kididdigar ayyuka ta SERAP ta shigar da ita kara.

A hukuncin da mai shari’a Deinde Deopelu ya gabatar a watan Yuni, ya ce tsohuwar Ministar ta fito ta bayyana hakikanin yadda ma’aikatar ta, ta kashe wadannan kudade, wajen zayyana sunayen wanda suka ci gajiyar kudaden, da Jihohinsu da kuma adadin kudin da aka tallafa musu.

Alkalin ya ce hukunci yazo daidai da yadda kundin tsarin mulkin kasar ya ba wa kowa damar samun bayanai, kuma hakan yasa ya umarci tsohuwar Ministar ta bayyyana wannan alkaluma ga kungiyar SERAP.

A hirarsa da Muryar Amurka Dakta Faruk Bibi Faruk Malami kuma Masanin kimiyyar Siyasa dake Jami’ar Abuja, ya ce “rashin bin diddigin yadda ma’aikatu ke gudanar da ayyukansu, yana daga cikin abinda ke jawo cin hanci da rashawa”

Idan za’a iya tunawa, a watan Disambar shekarar da ta gabata, Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gayyaci tsohuwar Minista Sadiya Umar Faruk domin amsa tambayoyi, haka ita ma wanda ta gaje ta Betta Edu, ta fuskanci dakatarwa bisa zarginta da karkatar da wasu kudade.

Saurari cikakken rahoton Rukaiya Bashar:

Kotu Ta Umarci Sadiya Umar Ta Bayyana Yadda Ta Kashe Naira Biliyan 729
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG