Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) tace tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, baya hannunta.
A sanarwar daya fitar a yau Laraba, mai magana da yawun hukumar efcc, Dele Oyewale, yace har yanzu ana neman tsohon gwamnan akan “zargin aikata almundahanar naira bilyan 80.2”.
“Babu gaskiya game da rahotannin da ake yadawa a kafafen yada labarai a yau na cewar wai tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello na hannun efcc. hukumar na son ta nanata cewar Yahaya Bello baya hannunta”.
“Har yanzu ana neman Yahaya Bello, mutumin da EFCC ta ayyana a matsayin wanda take nema akan tuhume-tuhumen halasta kudaden haram har naira biliyan 80.2, kuma akwai sammacin kama shi daga kotu”, a cewar oyewale.
Matsayar EFCC ta ci karo data ofishin yada labaran Yahaya Bello dake cewar tsohon gwamnan ya mutunta gayyatar hukumar.
Sanarwar da daraktan ofishin yada labaran Yahaya Bello, Ohiare Micheal, ya fitar a yau Laraba, tace tsohon gwamnan ya amsa gayyatar EFCC “bayan tuntubar iyalansa da tawagar lauyoyi da kuma abokansa na siyasa.”
Dandalin Mu Tattauna