Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yankewa Wasu Sojoji Hukuncin Laifin Fyade a Sudan Ta Kudu


Wata Kotun sojin Sudan Ta Kudu, jiya Alhamis, ta zartas da hukunin daurin shekaru 10 ma wasu sojoji saboda laifin yin fade ma wasu 'yan kasashen waje ma'aikatan agaji da kuma kashi wani dan jaridar kasar a wani mummunan harin da su ka kai a otan din Terrain shekaru sama da biyu da su ka gabata.

Kotun ta kuma umurci gwamnati da ta biya diyya ga wadanda harin na ran 11 ga watan Yulin 2016 ya rutsa da su. Sojojin gwamnati sun fafata ba ji ba gani na tsawon kwanaki uku da dakarun da ke biyayya ga tsohon Mataimakin Shugaban kasa Riek Machar.

Babban alkalin kotun ta soji Burgediya-janar Knight Baryano ya yanke ma wasu sojoji biyu hukuncin daurin rai da rai, wasu biyu kuma an yanke masu fursunan shekaru 14, sanan wasu sojoji biyar daurin shekaru 10 aka yanke masu.

An saki wani soja saboda rashin hujja. Kwamandan da ake zargi da jagorantar harin ya mutu a gidan yari tun a watan Oktoban bara, a wani al'amarin da sojoji su ka kira "mutuwar da aka saba gani."

Kotun ta kuma umurci gwamnati ta biya diyyar shanu 51 ga iyalin dan jaridan da aka kashe, John Gatluk, ma'aikacin wani Gidan Rediyon Al'umma.

Alkali Baryo ya kuma umurci gwamnatin Sudan da ta biya kowanne daga cikin wadanda aka yi wa fade diyyar dala $4,000 ta kuma biya mai otal din Terrain sama da dala miliyan biyu a matsayin diyyar barna.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG