Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangantakar Habasha Da Eritrea Na Kara Karfi


Fara Ministan Habasha, Abiy Ahmed.
Fara Ministan Habasha, Abiy Ahmed.

Fara Ministan Habasha Abiy Ahmed, yayi tafiya zuwa kasar Eritrea, ziyararsa ta farko tun da kasashen biyu makwabtan juna, suka kawo karshen gabar shekaru 20 dake tsakaninsu a watan Yulin bana.

Ministan labaran Eritrea, Yemane Meskel, ya fada ta kafar Twitter cewa, Fara Minista Abiy ya sauka ne a birnin Assab, inda shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya taryeshi. Daga bisani kuma suka tafi babban birnin Asmara.

Sashen kuryar Afirka na Muryar Amurka ya rawaito cewa shugaba Abiy ya ziyarci Massawa, inda a karon farko cikin shekaru masu yawa jirgin ruwan Habasha ya tsaya a Eritrea, yana daukar ma'adinai da aka hako a Eritrean.

Fara Ministan Habashan dai zai yada zango har kwanaki biyu a Eritrea, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gida daga taron kolin China da kasashen Afirka a birnin Beijing.

Shima shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed ya kai ziyara birnin Asmara, domin shiga taron da Abiy da Afwerki ke yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG