Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Habasha ta Sake Bude Ofishin Jakadanci a Eritrea


Shugaba Abiy Ahmed tare da Shugaba Isaias a yayin bude ofishin jakadancin Ethiopia a Eritrea.
Shugaba Abiy Ahmed tare da Shugaba Isaias a yayin bude ofishin jakadancin Ethiopia a Eritrea.

Alaka mai karfi na kara kulluwa tsakanin Ethiopia da Eritrea bayan shekaru 20 da lalacewar dangantakar kasashen biyu.

Kasar Habasha ta sake bude ofishin jakadancin ta dake Eritrea, wannan ne mataki na baya baya na kara karfafa dangantakar da ta tabarbare tsakanin kasashen har ta janyo tashin hankalin da aka kwashe shekaru 20 ana yi.

Kafar yada labaran Fana da ke da alaka da gwamnati, ta fada a yau Alhamis cewa Firai Minista Abiy Ahmed, ya sake bude ofishin jakadancin kasarsa a babban birnin Eritrea, wato Asmara, a wani takaitaccen biki da aka yi da Shugaba Isaias Afwerki. Shugabannin biyu za su yi wani taron koli na bangarori uku tare da Shugaban Somaliya, Mohamed Abdullahi Mohamed daga baya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG