Wata kotu ta wanke tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak daga duk wasu caje caje da suka kunno kai daga zargin cewa da hannunsa a kashe masu zanga zanga a lokacin juyin juya halin shekara ta dubu biyu da goma sha daya data hambarar da gwamnatinsa.
Yau Asabar aka yanke wannan hukunci. Wani alkali ya dauki lokaci yana bayani a kotun data cika makil da mutane kafin ya bada sanarwar cewa an wanke shugaban daga dukkan caje caje da ka yi masa.
Nan da nan mutane dake cikin kotun suka buge da murna bayan da aka bada sanarwar hukuncin. 'Ya'yan Mr. Mubarak da wadanda ake zargin su tare, sai suka sumbaci tsohon shugaba a goshinsa a yayinda yake sauraron hukuncin da aka yanke.
A hukuncin daya dade yana karanta, alkali yayi kira ga 'yan jarida da kada su rubuta nazari ko rahoto akan wannan hukunci har sai sun karanta bayani mai shafi dubu daya da dari hudu da talatin daya baiyana abinda yasa aka dauki wannan mataki.
Su ma Ministan harkokin cikin gida da manyan jami'an tsaro guda shidda wadanda suma aka zarga da laifin bada umarnin a harbe masu zanga zanga, suma an wanke su.
A zargi Mr. Mubarak da sauran jami'an da laifin bada umarnin kashe daruruwan masu zanga zanga.
Haka kuma an wanke tsohon shugaban dan shekara tamanin da shidda daga zarge zargen cin hanci da rashawa tare da 'ya'yansa Alaa da Gamal. To amma duk da haka a halin yanzu yana hukuncin daurin shekaru uku akan cajin yin almubazaranci da kudin jama'a na dabam.
shugaban wanda ya jagorancin ragamar mulki har na kusan shekaru talatin, a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu, aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Shekara daya bayan an yanke wancan hukunci, wata kotun daukaka kara tayi watsi da hukunci, aka sake yin shari'a.
Tun wancan lokacin aka yi masa daurin talala, a wani asibitin soja.
Yanzu haka dai tsohon shugaban jami'an tsaro a karkashin gwanatin Mubarak, Abdel Fatah El Sisi ne shugaban Masar.