Hukumomi a Masar suka ce hare hare biyu da aka kai a zirin Sinai ya halaka akalla jami’an tsaro 28 , a wani mummunar tarzoma a kasar tun bayan da sojoji suka hambare shugaba Mohammed Morsi mai ra’ayin addini a bara.
Jami’ai suka ce akalla sojoji 25 ne suka mutu a harin na farko lokacinda wani bam da aka boye cikin wata mota ta tashi a wani wurin duba motoci da sojoji suka kafa kusa da wurin da ake kira al-Arish.
A harin na biyu kuma, ‘yan binidga suka bude wuta a wani wurin duba motoci kusa da al-Arish, gari mafi girma zirin mai fama da rigingimu.
Jami’an Masar suka ce wasu fiyeda 25 kuma sun jikkata a hare haren.
Babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin harin da aka kai jiya jumma’a, a jerin hare hare da ake ta kaiwa kan jami’an tsaro a Masar, galibinsu a zirin na Sinai.