Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmi da Kirista Sun Yi Bude Baki Tare a Abuja


Musulmai na shirin sallah a Abuja
Musulmai na shirin sallah a Abuja

Cibiyar zantawa tsakanin musulmi da kirista ta masallacin Juma'a dake anguwar 'yan majalisa ta shirya bikin bude baki tare da kirista a masallacin.

Wakilin shugaban darikar Katolika na Abuja Reverend Roland yace babbar misali ne a hudubar Annabi Muhammed (S.A.W) ta bankwana inda yake cewa kar ka cutar domin kada a cutar da kai.

A nazarin Father Roland Musulunci na koyas da adalci ne ba tashin hankali ba. Yace wasu sun nuna damuwa lokacin da ya fada masu zai zo masallacin har ma suna cewa shin ko ya sanar da shugaba Jonathan. Amma yace shi ya san kalau zai koma domin ko a zamansa a Masar ana gayyatarsa zuwa masallaci su taka rawa irin ta musulunci.

A jawabinsa shugaban hukumar wayar da kan jama'a Mike Omeri ya tuno tasowarsa a Maiduguri inda yace a lokacin sallar Musulmi akan saya masu kaya a kasuwar Monday Market wacce a halin yanzu ake sawa bamabamai. Inji Omeri muamalar Musulmi da Kirista a lokacin tamkar 'yanuwa ne. Yayi fatan hakan zai dawo.

Jagoran kungiyar Imam Nuru Khalil yace ya halarta Musulmi yu shiga majami'a. Musulmi zai iya zuwa coci a yi hulda dashi ta zaman lafiya. Duk abun da yake na alheri ne idan aka gayyaci Musulmi zuwa coci zai iya zuwa. Yace duk Musulmi yakamata yayi kokari yayi wani abu domin a kawar da zargin da ake cewa Musulmai 'yan ta'ada ne, masu kashe mutane ne ko masu yin kaza da kaza. Amma sai an yi hakuri an yi aiki tukuru kafin a kaiga wannan matsayin.

Dattawa maza da mata na Musulmi da Kirista sun halarci taron inda har ma Kirista suka dinga raba abincin bude baki.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG