Shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sissi ya ce harin da aka kaiwa wani shingen sojoji na duba matafiya a mashigin Sinai wanda ya hallaka sojoji 30, aiki ne da aka aitawar da taimakon kudaden kasashen waje, sannan ya ce dole ne a rataye wadanda ke aikata irin wadannan hare-hare.
A jiya Asabar Mr.el-Sissi yayi alkawarin daukan matakai masu gauni akan 'yan tawaye, ya ce akwai manyan kasashen wajen dake neman durkusar da kasar Masar, kuma ya ce kasar shi ta kaddamar da yakin da za ta dade ta na yi da irin wadannan.
Gwamnatin kasar Masar ta kafa dokar ta bacin wata uku a yankunan arewaci da kuma tsakiyar mashigin na Sinai, sannan kuma bayan wasu hare-haren ta'addanci guda biyu da aka kai ran Jumma'a, gwamnatin ta kasar Masar ta ce ta rufe kan iyakar Rafah wadda ake tsallakawa zuwa Gaza.