Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kawo Karshen Tafsirin Azumin Bana a Abuja


Sultan Muhammadu Saad Abubakar III Mai Martaba Sarkin Musulmi
Sultan Muhammadu Saad Abubakar III Mai Martaba Sarkin Musulmi

An kawo karshen tafsirin azumin bana a yankin babban birnin tarayyar Najeriya Abuja da yiwa kasar addu'o'i na musamman.

Muhammed Ibrahim Duguri ya bayyana tafsirin bana da aka gabatar a yankin Abuja a wani da aka yi cikin nasara.

Yace sun yi yaki da duk abun da zai kawo ma jama'a zaman banza domin rashin abun yi ke hana alamura su cigaba. Rahotanni daga duk wuraren da aka tura malamai su yi tafsiri su ma sun bayyana samun nasarori.

Tun da aka soma azumi manyan malamai suka dinga yin tafsiri a sassa daban daban na yankin Abuja. Sun aika sakonnin neman dorewa kan ibada da yiwa kasar addu'ar dawowar salama musamman a yankin da ake asarar rayuka kusan kullum.

An kira a yi anfani da damar da aka samu a roki Allah Ya dawowa kasar zaman lafiya. Dr Abubakar Hassan Dikko shi ya gabatar da tafsiri a masallacin Maitama. Yayi misali da zamanin wani shugaba a Masar Isma'ila Kilili wanda ya tara malamai suka yi mako daya suna karanta Sahilul Buhari domin neman lafiya ga fitinar da ta auku irin wacce Najeriya ke fama da ita yanzu. Amma ba'a samu salamar ba sai da daya daga cikin malaman yayi ta maza ya fadawa sarkin gaskiyar lamarin wadda ta kai aka kirashi fada da yiwuwar daukan kowane irin mataki a kansa.

Malamin ya fadawa shugaban ko su yi adalci domin Allah ya kawo masu salama ko su ki Allah kuma ya saukar masu da masifar da zata fi karfin rayuwarsu. Malamin yace idan bai fadi gaskiya ba Allah zai tambayeshi. Sarkin ya yadda ya dauki matakan adalci da tsaro kasar kuma ta gyaru. Dr Dikko yace ya shugaban kasar Najeriya ko baka jin Hausa wannan labari ne gareka.

A masallacin Wuse II Sheikh Husseini Zakariya ya rufe tafsirinsa da kiran a gujewa haramta halal

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG