Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Bukaci Bayani Kan Naira Biliyan 206 Da Aka Cusa A Kasafin Ma’aikatar Jinkai Na 2023


Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Majalisar Dattawa)
Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Majalisar Dattawa)

Wani zargi na cushe a kasafin kudin Ma'aikatar Jinkai da Agaji da magance bala'i da ci gaban al'umma, ya sa kwamitin Majalisar Dattawa da ke kula da ayyukan na musamman, a karkashin Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, gayyatar Ministar Kudi da tsare-tsare, Zainab Shamsunah Ahmed, don bayani.

ABUJA, NIGERIA - An dai gayyaci Ministar Kudi Zainab Shamsunah Ahmed ne domin ta yi bayanin yadda aka saka Naira biliyan 206 a cikin kasafin kudin shekara 2023 na Ma'aikatar ta Jinkai.

Ministar Kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed (Instagram/ Zainab Shamsuna
Ministar Kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed (Instagram/ Zainab Shamsuna

An zartar da kudurin gayyatar Ministar ne yayin wani zama na musamman na kare kasafin kudi na Ma'aikatar Kula da Agaji da Jinkai ta kasa.

Hakan ya biyo bayan gazawar da Ministar Agajin Sadiya Umar Farouk ta yi, wajen bayar da bayanai kan yadda aka samu kudi, wuri na gugan wuri har Naira biliyan 206 a cikin kasafin kudin Ma'aikatarta na shekara 2023.

A lokacin da ta ke amsa tambayoyin daga kwamitin Sadiya Umar Farouq ta yi zargin cewa ba ta san yadda ma'aikatar kudi ta saka Naira biliyan 206 a cikin kasafin kudin ma'aikatar ta ba.

Sadiya Umar Farouq
Sadiya Umar Farouq

Sadiya ta ce a kasafin kudin ta na bana akwai wasu kudade da ta nema domin Hukumar Bunkasa Yankin Arewa Maso Gabas ta gudanar da wasu muhimman ayyuka, amma ma'aikatar kudi ba ta sakar mata kudaden ba.

Sadiya ta ce ta yi mamakin yadda aka cusa wadannan kudade a kasafin kudin ma'aikatarta.

Yaya za a zargi ma'aikatar kudi da yin cushe a kasafin kudin wata Ma'aikata?

Shugaban kwamitin kula da ayyuka na musamman Sanata Yusuf Abubakar Yusuf ya yi karin bayani cewa ma'aikatar kudi ita ce take yin bitar dukkannin kasafi da ma'aikatu da hukumomin gwamnati ke yi kafin Shugaban kasa ya kai ga gabatar wa Majalisar Dokokin kasa da kasafin kudin na shekara.

Yusuf Abubakar Yusuf
Yusuf Abubakar Yusuf

Saboda haka ma'aikatar kudi ce za ta san yadda aka yi wadannan kudade har Naira Biliyan 206 suka shiga kasafin kudin ma'aikatar agaji da Jinkai.

Gwamnatin Tarayya, a ta bakin Atoni Janar na kasa Abubakar Malami, ta nuna takaicin ta akan irin wannan cushe da ke faruwa da kasafin kudin ma'aikatu da hukumomin gwamnati.

Ministan Shari'a Abubakar Malami (Facebook/Abubakar Malami)
Ministan Shari'a Abubakar Malami (Facebook/Abubakar Malami)

Malami ya ce yin cushe a kasafin kudi abu ne da ya kamata a tunkare shi da dukkan karfi; a yake shi domin yana kawo ci baya a harkokin gudanar da ayyukan more rayuwa.

Malami ya kuma ce cigaba ake so a kasa irin Najeriya da ke da bukatu daban-daban, saboda haka za a hada karfi da karfe wajen yakan cushe da ke yawan faruwa a kasafin kudin kasar.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:

Majalisar Dattawa Ta Bukaci Bayani Kan Naira Biliyan 206 Na Ma’aikatar Jinkai Dake Kasafin 2023.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

XS
SM
MD
LG