Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Akan Wani Dan Kasar Denmark Saboda Hallaka Mata Da 'Yarsa


Peter Nielsen da matarsa da 'yarsu
Peter Nielsen da matarsa da 'yarsu

Kotun Daukaka Kara dake zamanta a Legas ta tabbatar da hukuncin kisa akan wani dan asalin denmark, Peter Nielsen, wanda aka yankewa hukuncin kisa a shekarar 2022 saboda hallaka matarsa ‘yar Najeriya, Zainab da diyarsu, Petra.

Kotun Daukaka Kara dake zamanta a Legas ta tabbatar da hukuncin kisa akan wani dan asalin Denmark, Peter Nielsen, wanda aka yankewa hukuncin kisa a shekarar 2022 saboda hallaka matarsa ‘yar Najeriya, Zainab da diyarsu, Petra.

Kotun ta yi fatali da karar da Nielsen ya daukaka gabanta saboda rashin hujja.

Da take zartar da hukuncin, Kotun Daukaka Karar tace wanda ake karar, gwamnatin jihar Legas ta gabatar da hujjoji na yankan shakku na aikata laifin kisan kai akan mai kara, Nielsen.

Don haka kotun ta baiwa wanda ake kara gaskiya tare da yin fatali da karar mai kara a hunkuncin data yanke.

A ranar 13 ga watan Yunin 2018, gwamnatin jihar Legas ta gurfanar da wanda ake tuhuma mai shekaru 53 da haihuwa a gaban kotu, akan tuhume-tuhumen kisan kai guda 2, wadanda sashe na 223 na kundin hukunta manyan laifuffuka na jihar Legas, na 2025, ya tanadi hukuncinsu, inda ya ayyana hukuncin kisa, matukar kotu ta samu mutum da laifi.

Wanda ake karar ya ki ya amsa laifinsa a tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Rahotanni sun bayyana cewar, Mr. Nielsen ya hallaka matarsa, Zainab wacce mawakiya ce kuma an fi saninta da Alizee, da diyarsa a ranar 5 ga watan Afrilun 2018 a gidansu da tsibirin Banana a shiyar Ikoyin jihar Legas.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG