Wannan lamari dai ya faru ne a daidai lokacin da damuna ke ci gaba da kankamawa a yankuna da daban-daban na Jamhuriyar Nijar.
An dai juma ba a ji duriyar ‘yan bindiga a kan iyakokin Nijar da Najeriya ba, inda suka afkawa al'ummar garin Dambu da ke cikin karamar hukumar Bazaga.
Hakimin garin Dambu Halidu Assoumane ya ce maharan sun shigo garin da kusan karfe goma sha biyu na daren ranar Asabar, inda suka shigo a kafa, kafin su bude wuta da manyan bindigogi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata wani da yake cikin mawuyacin hali yanzu haka a asibitin Galmi.
Ya ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da dukiya mai yawa da suka hada da rakuma da shanu kafin jami’an tsaro su isa wurin.
A kwanakin baya dai shugaban gundumar Birni N’Konni, kuma shugaban majalisar tsaron wannan yanki, Kaptin Abubakar Ali Shina, ya yi kira ga mutanen garuruwa da ke kan wadannan iyakokin da su dauki matakan kula da abin da ke kai komo da ma kariya, kamar irin yadda babban birnin yakin na N’Konni ya kafa kwamitocin ‘yan kato da gora, domin samun damar kare kai tare da gaugauta sanar da jami'an tsaro.
Shi ma masanin harakokin tsaro, Malam Yusha'u Abdullahi, ya ce yana da kyau mutanen garuruwan da ke wannan yankin su kafa kwamitocin tsaro don kare garuruwan su, kamar yadda makwabtansu na Najeriya ke yi, wanda da zarar sun ga motsi abun da ba su yarda da shi ba su gaggauta sanarwa da jami’an tsaro don su kawo musu dauki.
Saurari cikakken rahoton Harouna Mamane Bako:
Dandalin Mu Tattauna