Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Katsina Ta Amince Wa Ma’aikata Mata Da Mazansu Suka Rasu Zaman Iddah A Gida


Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda

Gwamnatin jihar Katsina ta bullo da dokar zaman Iddah ga mata ma’aikatan gwamnati tsawon watanni hudu da kwana goma idan sun rasa mazajensu.

A Musulunci ana yin iddah ne lokacin da mace ta rasa mijinta ko suka rabu.

Gabatar da sabuwar dokar ta biyo bayan wani kuduri da majalisar dokokin jihar ta gabatar, inda ta bukaci gwamnatin jihar da ta duba batun wa’adin Iddah wanda hukumar zartaswa ta amince da shi, tare da yin aiki da shawarwarin da ‘yan majalisar zartaswa suka gabatar.

Shugaban ma’aikatan jihar Katsina, Alhaji Falalu Bawale ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.

Ya kuma kara da cewa, tuni aka tura takarda ga dukkan ma’aikatu da sassa da hukumomin jihar domin bai wa ma’aikata mata damar gudanar da zaman Iddah a lokacin da bukatar hakan ta taso.

“Mun yanke shawarar gabatar da wannan batu a gaban Majalisar Dattawa ta kasa domin a shigar da ita cikin ka’idojin aikin gwamnati inda matan da suka rasa mazajensu za a bar su su zauna a gida, su yi zaman Idda bayan mutuwar mazajensu.

“Majalisar ta ce, duk jihohi suna da ‘yancin zuwa su kirkiro dokar da ta dace da manufofinsu.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG